10 Nuwamba 2020 - 13:10
Ministan Harkokin Wajen Kasar Faransa Ya Ziyarci Jami’ar Azhar Ta Kasar Masar A Kokarin Da Yake Yi Na Sama wa Kasarsa Mafita

Ministan Harkokin Wajen Kasar Faransa Ya Ziyarci Jami’ar Azhar Ta Kasar Masar A Kokarin Da Yake Yi Na Sama wa Kasarsa Mafita

ABNA24 : Ministan harkokin wajen na kasar Faransa Jean Y-Yves Le Darian yana son sama wa kasarsa mafita daga matsalar da ta jefa kanta a ciki na cin zarafin ma’akin Allah, annabi Muhammadu ( S.A.W.).

Bayan ganawa da ya yi da shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi, da takwaransa Sameh Shukri, ya kuma gana da shugaban cibiyar Azhar, Sheikh Ahmad al-Tayyib.

Ministan harkokin wajen na Faransa ya fadawa shugaban cibiyar ta Azhar cewa; Kasarsa tana matukar girmama addin musulunci.

Sake buga zanen cin zarafi ga addinin musulunci da kuma kiran da shugaban kasar Faransa Macron ya yi na cewa; Dole a yi wa addinin musulunci kwaskwarima sun jefa kasar cikin sa-in-sa da duniyar musulmi, inda ake yin kiraye-kirayena a kauracewa kayan da Faransan take kerawa.

342/